Turkiyya ta kaddamar da atasaye soji a yankunan tekun Ejiye da Bahar Rum kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar.
Ma’aikatar ta kara da cewa jiragen Ruwan Rundunar sojan ruwan Turkiyya da jiragen masu saukar ungulu na yaki suna ci gaba da gudanar da atisayen hadin gwiwa a yankunan tekun Ejiye da Bahar Rum.
Hankula dai sun kara tashi a yankin Bahar Rum sabili da yadda Turkiyya da Girka suka rinka atasayen soji a yankin Bahar Rum. A ranar Alhamis Faransa zata taya Girka, Cyprus bangaren Rum da italiya a atasayen kwanaki uku a yankin Bahar Rum.
A ranar Alhamis Girka ta bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta aika da jiragen yaki hudu da jiragen daukar sojoji biyar a tsibirin Crete domin ci gaba da atasayen sojoji da Girka.
Turkiyya dai ta kalubalanci Girka akan kokarin mallakae tsibirin ita tilo wanda bata da hakki sabili da haka tsibirin bai kamata ya kasance daga cikin yankin da za’a lissafa tsakanin kasashe ba.
Haka kuma Ankara na ci gaba da kalubalanatar Cyprus ta bangaren Roma akan ayyukan hakar ma’adanai da take yi ita tilo a yankin Gabashin Bahar Rum, inda ta bayyana cewa Jamhoriyar Cyprus banagaren Turkiyya m anada hakki akan albarkatun kasas dake yankin.