Turkiyya da Yukiren sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a fagen samar da tsaron sararin samaniyya.
Masana'antar Kayan Lantarki ta Soja (ASELSAN) da kamfanin shigo da makamai na kasar Yukiren Ukrspetseskport sun rattaba hannu kan yarjejeniya kan zamanantar da tsarin tsaron sararin samaniya.
A cikin sanarwar da kamfanin tsaron kasar Yukiren Ukroboronprom ya bayar, an ba da rahoton cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a baje kolin masana'antar tsaron kasa da kasa (IDEF 2021) da aka gudanar a Istanbul.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa kamfanonin biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a fannin zamanantar da tsarin tsaron sararin samaniya, kuma an bayyana cewa Babban Manajan kamfanin, Vadim Nozdriya, ya lura cewa yarjejeniyar wani sabon mataki ne na ci gaba na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe a fannin fasahar soji.