Kasashen Turkiyya da Kazakhstan sun bayyana niyyar bunkasa hadakar kanfunan tsaron dake tsakaninsu.
Kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar Kazakhstan ta sanar mataimakin ministan tsaron Turkiyya Muhsin Dere ya gana da ministan tsaron Kazakhstan Nurlan Yermekbayev a yayinda ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Kazakhstan.
A ganawar an tattauna akan hadakar harkokin tsaro da kuma yarjejeniyar horas da sojoji dake tsakanin kasashen biyu.
Kazakhstan da Turkiyya zasu ci gaba da bunkasa huldan dake tsakaninsu ta ko wace fani.
Haka kuma a taron an tabo batun inganta hadakar kanfunan tsaro dake tsakanin kasashen biyu.
Dere tare da tawagarsa sun kuma gana da ministan harkokin kanfuna da cigaban kasar Kazakhstan Beibut Atamkulov.