Ministan harkokin wajen Turkiyya ya aike da sakon jaje ga takwaransa na Girka kan gobarar daji da ta barke a kasar a cewar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya.
A wayar tarho, Mevlut Cavusoglu ya isar da jajen Turkiyya da fatan kawo karshen masifar cikin kankanen lokaci ga takwaransa na Girka Nikos Dendias.
Ita ma kasar Turkiyya na ci gaba da fama da ayyukan kashe gobarar dajin a cikin kwanakin nan.