Turkiyya da Amurka na tattaunawa akan kare filin jirgin saman Kabul

Turkiyya da Amurka na tattaunawa akan kare filin jirgin saman Kabul

Hadakar da ke tsakanin Turkiyya da Amurka kan tsaron filin jirgin saman Kabul na kasa da kasa bayan ficewar Amurka za ta ci gaba, in ji Ministan Tsaron kasa na Turkiyya.

"Babu wata matsaya da aka cimma a wannan lokacin," in ji Hulusi Akar ga manema labarai bayan ziyarar da ya kai Kyrgyzstan da Tajikistan.

“Za mu tattauna a taron da shugabanmu zai jagoranta. Kuma za mu sanya shirin ya fara aiki bayan amincewar shugaban kasa”

Wata tawaga ta Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da jami’an Pentagon sun isa Ankara a makon da ya gabata don tattaunawa kan ci gaban da aka samu kan kokarin ci gaba da aiki da Filin jirgin saman Hamid Karzai da ke Kabul bayan ficewar sojojin Amurka, wanda za a kammala shi a ranar 11 ga watan Satumba.

Daga baya bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa, kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta sanar.


News Source:   ()