A duniya baki daya, Turkiyya ce kasa ta 8 wajen yin allurar riga-kafin Corona (Covid-19).
Ya zuwa yanzu a duniya baki daya an yi allurar riga-kafin Corona sama da biliyan 4 da miliyan 180.
Bayanan da aka samu daga majiyoyin sanya idanu kan allurar riga-kafin Corona a duniya sun bayyana cewa, China ce a kan gaba wajen yin allurar sama da kwaya biliyan 1 da miliyan 670.
Indiya ce ke biyewa China baya da allurai miliyan 472 da dubu 220, Amurka na da miliyan 346 da dubu 460, Barazil kuma ta yi allurai miliyan 142 da dubu 490, Jamus miliyan 92 da dubu 50, Japan miliyan 87 da dubu 380, Ingila miliyan 85 da dubu 200 sai Turkiyya da ta yi allurai sama da miliyan 73 da dubu 616.
Haka zalika alkaluman sun bayyana cewa, Faransa ta yi allurai miliyan 72 da dubu 670, Italiya miliyan 68 da dubu 740, Indonesiya miliyan 68 da dubu 150, Mekziko miliyan 67 da dubu 360, Rasha miliyan 62 da dubu 230 sai Spaniya da ta yi allurai miliyan 56 da dubu 190.