Kamfanin jiragen saman Turkiyya (Turkish Airlines) ya dakatar da zuwa Tel Aviv Babban Birnin Isra'ila sakamakon dalilai na tsaro.
Kamfanunnukan jiragen sama da dama sun dakatar da zuwa Isra'ila sakamakon hare-haren da take kaiwa Zirin Gaza.
An soke tashin jirgin saman Turkish Airlines daga Istanbul zuwa Tel Aviv da safiyar Juma'ar nan saboda dalilai na tsaro.
Matakin da aka dauka ya shafi jiragen ranakun Asabar da Lahadi.