Turai na shirin girke jami’an sojinta a Ukraine

Turai na shirin girke jami’an sojinta a Ukraine

Tattaunawar tura sojojin wadda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bijiro da ita, tana nan a matakin farko, amma tuni ta fara haddasa rarabuwar kawuna tsakanin ƙasashen na EU, inda wasu daga cikinsu ke ganin cewa, bai kamata a kaddamar da wannan zance a yanzu ba.

Duk da cewa, Ukraine na ɗanɗana kuɗarta a yaƙinta da Rasha a yanzu, amma shugabannin ƙasashen Turai na ƙoƙarin kauce wa duk wani abu da zai sa shugaba Vladimir Putin ya ji a ransa cewa, ana rarrashin sa ne don ya shiga tattaunawar sulhu.

A maimakon haka, sun dage kan cewa, sun mayar da hankali ne wajen bunƙasa agajin soji da tattalin arziƙi ga Ukraine, a yayin da suke ganin cewa, babu wata alama da ke nuna shugaba Putin a shirye yake ya shiga tattaunawar sulhun don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

Sai dai duk da haka, har yanzu akwai wasu hukumomi a bayan fage da ke duba yiwuwar yadda ƙasashen na Turai za su samar da garantin tsaro ga Ukraine, koda kuwa ta hanyar girke dubun dubatan sojoji ne a ƙasar.

Matakin aikewa da sojojin na a matsayin barazanar fito-na-fito tsakanin Rasha da Turai wadda tuni rumbun ajiyar makamanta ya rame sakamakon jerin tallafin da ta yi ta bayarwa na makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)