Ma'aikatar harkokin lafiyar kasar Tunisia ta sanar da kara wa'adin dokar hana fita waje na makonni biyu domin kara daukar matakan hana yaduwar kwayar cutar Korona.
Mai magana da yawon ma'aikatar lafiyar kasa Nassaf bin Aliyye ya shaidawa manema labarai da cewa kasar ta kara daukar wasu matakan dakile kwayar cutar Covid-19.
Bisa ga dokar han fita waje an kara wa'adin har zuwa ranar 11 ga watan Afirilu inda Aliyye ya kara da cewa dokar na aiki ne tsakanin karfe 22.00 zuwa karfe 06.00 na safe.
Aliyye ya ja kunne da cewa idan aka samu yankunan da aka samu karin yawan masu kamuwa da cutar za'a saka dokar hana fita waje baki daya.