Tudun kankara na gab da karo da Tsibirin South Georgia da ke Ingila

Tudun kankara na gab da karo da Tsibirin South Georgia da ke Ingila

Birtaniya ta yanke shawarar tura wata tawagar bincike zuwa tudun kankara wanda ke dab da karo da Tsibirin South Georgia.

Tudun kankaran mai suna A68a ya fara tafiya arewa tun lokacin da ya balle daga kan tudun kankara mai suna Larsen C da ke Antarctica, a shekarar 2017.

Tudun kankaran, wanda ke da fadin kilomita dubu 3 da 900, yana a nisan kusan kilomita 75 daga tsibirin.

Babu mazauni na dindindin a South Georgia a lokacin hunturu amma akwai akalla mutane 30 da ke zama a tsibirin a watannin bazara.

An kiyasta cewa tsuntsaye miliyan 30, gami da tsuntsaye nau'in penguin miliyan bakwai, da wani nau’in dabba na karkashin ruwa da ake kira seal miliyan biyu suna rayuwa a tsibirin.

Masana sun bayyana cewar ruwa marasa gishiri da ke narkewa daga tudun kankaran zai yi mummunan tasiri ga dabbobi da rayuwar abubuwan teku a yankin.

Masana sun kuma bayyana cewar bayan tudun kankaran ya yi karo da tsibirin, sarkar abinci a yankin za ta tabarbare.

Ana sa ran tawagar bincike daga Cibiyar Bincike ta Antarctica ta Birtaniya za ta koma yankin a karshen watan Janairu.

Tawagar za ta tattara bayanai daga yankin kamar yanayin zafin ruwan tekun, adadin gishiri da ke tekun da kuma yawan abubuwa masu rai a cikin ruwan.


News Source:   ()