Tuddan dusar kankara sun ruguzowa mutane a Afganistan

Tuddan dusar kankara sun ruguzowa mutane a Afganistan

Mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon ruguzowar tuddan dusar kankara a jihar Badahshan da ke arewa maso-gabashin Afganistan.

Kakakin Fadar Gwamnan Badahshan Nik Muhammad Nazari ya shaida cewa, mutane 14 sun mutu sakamakon fado musu da tuddan dusar kankara suka yi a gundumar Rajistan da ke lardin Badahshan.

Nazari ya kara da cewa, wasu mutanen 4 sun jikkata a ibtila'in kuma akwai yiwuwar akwai wasu mutanen a karkashin dusar kankarar kuma ana ci gaba da aiyukan ceto a wajen.

 


News Source:   ()