Tsohuwar ministan harkokin wajen Isra'ila ta soki matakin kasarta akan Gaza

Tsohuwar ministan harkokin wajen Isra'ila ta soki matakin kasarta akan Gaza

Tsohuwar ministan harkokin wajen Isra'ila Tzipi Livni ta bayyana cewa mamayar yankin Zirrin Gaza zai kasance babban kuskure a tarihance wanda zai gurbatar da zaman lafiyar da ake tsamani za'a iya samu a yankin.

Livni, ta kasance tare da kafar talabijin din CNN inda ta yi hira da Christine Amanpour.

A yayinda aka tambayeta game da yunkurin da Isra'ila ke yi na mamaye Zirrin Gaza, Livni ta kada baki ta ce,

"Mamaye kusan kashi 30 cikin darin Zirrin Gaza da Isra'ila ke yunkurin yi zai kasance abinda zai gurbata zaman lafiyar yankin wanda ake fatan samu. Ko shakka babu wannan ba mataki ne da zai kare muradin Isra'ila ba"

Livni wacce ta aminta da kafa kasa biyu tsakanin Isra'ila da Falasdin ta yadda za'a zauna lamun lafiya a matsayar makota biyu ta kara da cewa,

"Wannan matakin gefe guda ba zai haifawa Isra'ila da mai ido ba. Kuma wannan zai kasance babban kuskure garemu, mu da muka yi amanna da samar da kasa biyu tsakanin kasashen biyu"


 


News Source:   www.trt.net.tr