An sanar da cewa tsohon shugaban Ulama'u ta kasa da kasa Yusuf Al-Karadavi mai shekaru 95 ya kamu da kwayar cutar Korona.
Karadavi ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa, ya fara samun kulawar kiwon lafiya bayan tabbatar da cewa ya kamu da covid-19.
Haka kuma an bayyana cewa Karadawi na cikin koshin lafiya inda aka nemi masuya su ci gaba da yi masa adu'a.
Dan cikin Karadawi, Abdurrahman Yusuf ma ya yada a shafukan sadar da zumunta da cewa mahaifinsa da aka yi wa allurar riga-kafin Korona ya kamu da kwayar cutar.