An yada hoton tsohon Ministan Tsaron Isra’ila Moshe Dayan yayinda yake satar kayayyakin tarihi a yankin Sinai dake Misira a shekarar 1969.
A wani rahoto da jaridar Isra’ila ta Maariv ta buga, an dauki hoton Moshe Dayan, wanda shi ne ministan tsaro na Isra’ila tsakanin shekarar 1967-1974, yayinda yake satar kayayyakin tarihi a yankin Serabit al-Hadim na tsibirin Sinai a Misira.
Rahoton, wanda aka bayyana cewa hoton ya tabbatar da cewa Dayan ya saci kayan tarihi, ya kunshi hotunan Dayan da sojojinsa dauke da jakunkuna cike da kayayyakin tarihin da suka wawure daga gidan adana kayayyakin tarihin Misira.