Tsigaggen shugaban Koriya ta Kudu ya yi wa jami’an tsaron da ke son kama shi tutsu

Tsigaggen shugaban Koriya ta Kudu ya yi wa jami’an tsaron da ke son kama shi tutsu

Akwai yuwuwar shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol da aka tsige ya fuskanci ɗauri a gidan yari ko ma hukuncin kisa zarar  jami’an tsaro suka samu nasarar kama shi, dukda a yanzu ya ja daga a cikin fadar shugaban ƙasa domin kaucewa kamu.

Shugaba Yool ya yi ƙememe ya miƙa wuya ga jami’an tsaro kawo yau Alhamis inda ya ce  a shirye yake ya yi faɗa da duk jami’an da ke buƙatar cika hannu da shi domin ya amsa tambayoyi dangane da dokar ta ɓaci da ya sanya a baya.

Magoya bayan Yoon sun yi zaman dirshan a wajen fadar shugaban ƙasar da aka tsige yayin da suma jami’an tsaronsa ke bashi cikakken tsaro cikin shirin ko ta kwana domin daƙile duk wani yunƙurin kama shi

Ƴan sanda sun yiwa fadar shugaban ƙasar zobe yayin da shugaba Yoon ya ɓuya kuma yaƙi nuna nadama, yayin da ake ci gaba da dambarwa tun bayan dokar ta ɓaci da ya sanya, ya kuma aike da saƙo ga magoya bayan shi kwanaki kafin umarnin da kotu ta bayar na kama shi ya ƙare a ranar 6 ga watan Janairu.

Lauyan shugaban ƙasar Yoon Kab-keun ya tabbatar da cewa shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige na cikin fadar shugaban ƙasa.

Tuni ƴan majalisa masu adawa da tsigaggen shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol su ka yi Allah wadai da matakin da ya ɗauka na tura saƙon ƙin amincewa a kama shi, inda mai magana da yawun jam’iyyar Democratic Party Jo Seoung-Jae ya ce yana ƙoƙarin kawowa ƙasar hargitsi.

Tuni tawagar lauyoyin Yoon Suk Yeols suka shigar da ƙara dake neman a dakatar da umarnin kama shi da aka yi, tare da cewa hakan ya sabawa doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)