Tsayin tsauni mafi girma a Sweden ya ragu

Tsayin tsauni mafi girma a Sweden ya ragu

Tsayin tsaunin Kebnekaise, tsauni mafi girma a Sweden ya ragu da mita biyu a cikin shekara guda.

An nuna wannan abun ban mamaki ta hotunan da aka dauka daga tauraron dan adam.

Dangane da bayanin da Sashen kula da yanayin ƙasa na Copernicus na Turai ya yi, gajartar ta afku ne sakamakon narkewar kankara.

Yayin da tsayin dutsen ya kai mita dubu 2 da 96 a bara, ya ragu zuwa mita dubu 2 da 94 a yanzu. A da, tsayin dutsen a ya kai har mita dubu 2 da 118 a tsakiyar shekarun 1990.

Masana kimiyya na tunanin tsayin zai ragu da rabin mita a tsakiyar watan gobe.

Ana kuma nanata cewa dumamar yanayi ta haifar da narkewar kankara kuma tana gab da kaiwa matsayin da ba za iya shawo kan ta ba.


News Source:   ()