Barkammu da wannan lokaci a cikin wani sabon shirinmu na sharhin alamurran yau da kullum. A wannan makon mun kasance tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA……
A yayinda Turkiyya ta dauki matakan da ba'a yi tsammani ba na yaki da kungiyar ta'addar PKK a yankin Gara dake Arewacin Iraki, ake ganin cewa Turkiyya za ta mayar da himma akan kalubalantar kungiyar ta'addar PKK a lraki da Siriya a cikin shekarar 2021. Kungiyar ta'addar PKK ta kasance karkashin matsin lamba a Turkiyya da lraki. Sai dai bangaren kungiyar dake Siriya wato PYD/YPG na ci gaba da zama babban kalubale ga kasar Turkiyya. Kungiyar da taimakon Amurka na yunkurin kafa gwamnatin ta'addanci a yankin.
Kungiyar ta'addar PKK ta hannun bangarenta a Arewacin Siriya ta yi amfani da damar yakin basasa da kasar ke ciki inda daga shekarar 2014 kawo yanzu ta rinka gwagwarmaya da Desh da kuma taimakon Amurka ta fadada ikonta a arewa maso gabashin kasar. Haka kuma karkashin SDG wacce za ta shafi tsattsar Larabawa ta rinka daukar matakan mallake ma'adanan kasar ta yadda za ta bunkasa tattalin arzikinta da zai ba ta damar kalubalantar tun daga gwamnatin Bashar Asad har izuwa Turkiyya, Rasha da lran. Gwamnatin Bashar Asad da ta fahinci muhimmancin mallakar maadanan kasar duk da matakan siyasar da ta dauka Amurka ta dakile yunkurin na ya, sabili da hakan ba ta samu wata nasara ba. Kasancewar ma'adanan kasar hannun kungiyar ta'adda lamari ne da Amurka ke taimakawa. Baya ga taimakawa ýan taadda da Amurka ta yi ta kuma yi dalilin taimakawa kungiyar SDG/YPG daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya.
Dangane ga bayanan tsaro da ake samu a cikin kwanakin nan kusan kaso kashi 30 cikin darin kasar Siriya wato sikwaya mita dubu 40, 000 na hannun SDG/YPG. Yankunan dake karkashin mallakar SDG/YPG yankuna ne masu gonaki masu inganci da kuma wurare masu dinbin arzikin man fetur, iskar gas da ruwa. Daga cikin sikwaya mita dubu dari hudu da muka ambata kaso 50 dinsa na tattare da ma'adanan makamashi, kaso 70 dinsa na da albarkatun ruwa wanda kuma kashi 95 cikin darinsa na hannun kungiyar ta'addar YPG.
Kungiyar PYD/YPG da ta bunkasa tattalin arzikinta da taimakon Amurka a yankin; ta na kokarin samun cikekken ýanci a yankin daga bisani kuma ta kafa kasar ta'addanci. Bugu da kari suna kuma yunkurin kara kai hare haren ta'addanci a yankin dake hannun kulawar Turkiyya da ma niyar fafatawa da Rasha da gwamnatin Bashar Asad in har ta samu dama.
Musanman bayan kaddamar da farmakin tafkin zaman lafiya a Siriya da Turkiyya ta yi ta kara bayyana kanta a matsayar wacce keda irin wannan nufin. Sai dai ko shakka babu Turkiyya ba za ta taba bada dama ga kungiyar ta'addar PKK a Turkiyya ko kuma ga barayinta a Siriya kafa gwamnatin ta'addanci ba. Bayan farmakin tafkin zaman lafiya da Turkiyya ta kaddamar a shekarar 2021 kuma ta fara daukar muhimman matakai na fatattakar kungiyar ta'addar a Siriya da Iraki. A bisa wannan tsarin ta na kuma yunkurin kauda yan ta'addan daga yankunan Tel Rifat, Menbich, Ayn lsa da Tel Temir. Hakan zai sanya kara karfafa sauran yankunan Larabawa da Kurdawa da kuma gurgunta 'yan ta'adda a yankin. A karshe dai, Turkiyya ba za ta taba rumgume hannu ta kyale kungiyar ta'addar PKK da sauran kungiyoyin dake karkashinta su dinga cin karensu ba babbaka a Turkiyya da a wasu makotanta kamar su Siriya da lraki ba.
Wannan sharhin Mal Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…