An sanar da cewa tsananin zafi ya yi sanadiyar rayukan mutum 148 a Tokyo babban birnin kasar Japan.
Kafar yada labaran kasar Japan ta NHK ta rawaito cewa Walin Tokyo ya yi jawabi akan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafi a birnin.
Akan hakan, a makon da ta gabata wasu mutum 17 sun rasa rayukansu tun farkon watan Agusta kawo yanzu mutum 148 suka rigamu gidan gaskiya sanadiyar tsananin zafi a birnin.
Sanarwar ta kara da cewa kaso 80 cikin darin wadanda suka rasa rayukansu a cikin mako guda 'yan sama da shekara 70, wadanda 14 daga cikinsu basu da na'urar bayar da iska a gidajensu.
Darajan zafi a birnin na Tokyo ya kasance a tsakanin daraja 32-37 daga watan Yuli kawo yanzu.