Sakamakon tsananin zafi a jihohin yammacin Kanada mutane 63 sun rasa rayukansu.
A rana guda sakamakon tsananin zafin mutane 63 ne suka mutu a garuruwan Surrey, Burnaby da Vancouver.
'Yan sanda sun bayyana cewa, mafi yawan wadanda suka mutu tsofaffi ne.
Zafi ya tsananta a yankunan British Columbia, Alberta, Yukon da Northwest Territories inda masana su ke kiran zafin da "kubbar dumama".
A wanni 34 da suka gabata tsananin zafi ya kafa tarihi da zama na 103.
A gefe guda, a fadin jihar British Columbia an samar da wuraren shan iska inda aka kunna manyan na'urorin bayar da iska ga jama'a a cibiyoyi da dama.
An rufe makarantu, gidajen sayar da abinci da kantinan saye da sayarwa a jihar, haka zalika an dage lokacin yin allurar riga-kafin Corona da ake yi wa jama'a.