Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 170 a Tokyo

Mutane 170 ne suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafi a Tokyo Babban Birnin Japan.

Ofishin Kula da Lafiya da Jin Dadin jama'a na Fadar gwamnan Tokyo ya fitar da sabbin bayanai game da wadanda tsananin zafi ya yi ajali a birnin.

Alkaluman da ofishin ya fitar sun nuna cewar karin mutane 22 masu shekaru tsakanin 60 da 90 sun sake mutuwa a cikin kwanaki 9.

Ofishin ya ce ya zuwa yanzu jimillar mutane 170 ne suka rasa rayukansu tsananin zafi a birnin.

Gwamnati ta shawarci mutane da su dinga shan ruwa sosai kuma su dinga samun iskar shaka yadda ya kamata.

Tun daga karshen watan Yuli zuwa yau darajar zafi a Tokyo ya kai 32 zuwa 37 a ma'aunin Celcius.


News Source:   ()