Asusun tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ne ya fitar da rahoton, inda ya ce a daidai lokacin da matsalar Sauyin Yanayi ke haddasa ƙaruwar yanayin zafi a faɗin duniya, a halin yanzu, yaro guda cikin biyar ne kwatankwacin yara miliyan 466 ne ke rayuwa a yankunan da ke fuskantar kwanakin tsananin zafin da adadinsu ya ninka sau biyu a duk shekara, idan aka kwatanta da abinda aka gani shekaru 60 da suka gabata.
Asusun na UNICEF ya yi amfani ne da kwanakin da aka riƙa fuskantar tsananin zafin da makinsa ya kai digiri 35 a ma’aunin Celcuis, a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024, gami da kwantanta yanayin da aka gani cikin shekarun 1960 zuwa kusan da 70.
Babban jami’in wayar da kan UNICEF Lily Caprani ta ce ya ƙara da gargaɗin cewa baya ga ƙananan yara, mata masu juna biyu ma na kan gaba wajen fuskantar haɗari daga tsananin zafin da ya yayi sanadin hana yaran miliyan 80 zuwa karatu saboda rufe makarantunsu da aka yi.
Rahoton ya ƙara da cewar ƙananan yaran da ke yammaci da tsakiyar Afirka ne suka fi fuskantar haɗari daga tsananin zafin domin kuwa adadinsu ya miliyan 123, idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI