Bayanan mujallar Cibiyar ta Barcelona Institude for Global Health sun nuna cewa tsanantar zafin da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, ya zarta na dukkanin lokutan da suka gabata da aka sani.
Cibiyar ta ci gaba da cewa a yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da haifar da tsananin yanayin zafi, yankunan Turai na cikin halin ha’ula’i, a yayin da al’ummar yankin da dama ke fuskantar ƙalubale na cututtuka mabambanta a sanadiyar zafin.
Yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da kara ta’azzara zafi, al’umar da ke yankin Turai na rayuwa ne a cikin mawuyacin hali a nahiyar da ke fuskantar ɗumamar yanayi sama da ko’ina a duniya, inda suke fuskantar barazanar rashin lafiya a sanadin tsananin zafi.
Masu bincike sun yi amfani da bayanan mace-macen da aka samu a sanadiyar yanayin zafi daga ƙasashen Turai 35, inda aka yi ƙiyasin cewa mutane dubu 47,690 ne suka mutu a sanadiyar wasu dalilai da ke da alaƙa da tsananin zafin.
A yayin da matsalar ta fi ƙamari a ƙasashe irinsu Girka da Bulgaria da Italiya da kuma Spain wadanda suka fi samun adadi mafi yawa na mace-mace masu alaka da zafin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI