A mako dayan da ya gabata mutane 23 sun rasa rayukansu sakamakon tsananin zafi da ake fuskanta a Japan.
Hukumar Kashe Gobara da Magance Ibtila'i ta bayyana cewa, a tsakanin 18 da 25 ga Yuli mutane dubu 8,122 ne suka je asibiti saboda tsananin zafi da ya buge su.
Hukumar ta ce 23 daga cikin mutanen sun mutu, sama da dubu 3 kuma na cikin mawuyacin hali.
Sama da rabin wadanda aka kai asibitin 'yan shekaru 65 zuwa sama ne, 'yan shekaru 18 zuwa 64 kuma su dubu 2,627 inda 800 kuma suke 'yan kasa da shekaru 17.
Kwararru na bayar da shawara kan a dinga kunna fanka idan zafi ya kai daraja 28 ko kuma danshin zafi ya kai daraja 70.