Tsananin zafi a Kanada ya haifar da gobarar daji

Tsananin zafi a Kanada ya haifar da gobarar daji

An bayyana cewa tsananin yanayin zafi a Kanada ya haifar da gobarar dajin da ya haifar da mace-mace a kasar.

Gobarar daji a yankin Lytton, kusa da lardin Kanada na British Columbia na barazana ga mazauna yankin.

An yanke shawarar kwashe mutanen yankin baki daya.

Mutuwar da aka samu sanadiyar matsanancin zafi wanda ya shafi yankunan yammacin Kanada, ya ninka mace-macen da aka saba samu a yankin har sau uku inda mutane 486 suka mutu a cikin kwanaki 5 da suka gabata.

Matsakaicin yanayi na baya-bayan nan ya kai digiri 49.9 a ma'aunin Celsius a garin na Lytton, kuma har yanzu yanayin zafin yana ci gaba a British Columbia da wasu sassan Alberta.


News Source:   ()