Tsananin sanyi da dusar ƙanƙara sun mamaye birnin Washington D.C na Amurka

Tsananin sanyi da dusar ƙanƙara sun mamaye birnin Washington D.C na Amurka

Wannan na faruwa yayin da ake zaman majalisa domin tabbatar da zaɓeɓɓen shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump.

Tsananin sanyin ya haddasa dusar ƙanƙarar mai zurfin inci 5 a babban birnin Amurka Washington DC.

Sai dai zurfin dusar ƙanƙarar ta kai inci 8 a sassan Maryland da VIRGINIA.

Ana hasashen cewar dusar ƙanƙarar za ta ci gaba da zuba a wannan rana har zuwa yammaci da ake sa ran za ta nufi cikin kogi a ranar litinin.

Dusar ƙanƙara ta mamaye birnin Washington D.C 02:13

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Dusar ƙanƙara ta mamaye birnin Washington D.C © Reuters

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)