Tsamo gawarwakin hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Ngaski dake jihar Kebbi a Najeriya

Ma’aikatan ceto masu zaman kansu na ci gaba da tsamo fiye da gawarwaki dari bayan kifewar kwale-kwale a cikin rafin Wara, helkwatan karamar hukumar Ngaski dake jihar Kebbi a arewa masu yammacin Najeriya.

A shekaran jiya ne a rafin Wara helkwatar karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi dake Najeriya aka samu hatsarin wani kwale-kwale dake dauke da kimanin mutum 160 wadanda suka hada da yara kanana da mata.

Kwale-kwalen ya dauko mutanen ne daga wani kauye dake jihar Neja karkashin karamar hukumar Borgo a jihar Neja inda ake tunon ma’adanai da suka hada da zinare da azurfa.

Kawo yanzu an tsamo gawarwaki fiye da 70 wadanda aka yi wa jana’iza, kamar yadda babban limamin Wara, helkwatar karamar hukumar Ngaski dake jihar Kebbi a Najeriya, Mal. Muhammad Musa ya bayyana.

A jiya gwamnan jihar Kebbi Alh. Atiku Bagudu da ya ziyarci karamar hukumar da iftila’in ya afku, inda ya gana da Mai Girma Sarkin Maginga Alh. Abdulmalik Nuhu da sauran shugabanin yankin akan daukar matakan kare afkuwar irin wannan lamarin a gaba.

Duk da dai kwale-kwalen da ya kifen sabo ne, ana sharhin cewa ya kife ne sabili da obalodin da aka yi masa ko kuma rashin amfani da ingantattun kayayyaki wajen kerashi kamar yadda shugaban karamar hukumar Ngaski Alh. Abdullahi Buhari Wara ya shaidawa manema labarai.

 


News Source:   ()