Shugaban Kungiyar Asayib Ahlulhak da ke karkashin tsagerun Hashdi Sha'abi 'yan Shi'a na Iraki Kays Hazali ya yi barazanar za su kashe sojojin Amurka don daukar fansa.
A jawabin da Hazali ya yi ta kafar talabijin ya tabo batun harin da Amurka ta kaiwa tsagerun Hashdi Sha'abi a iyakar Iraki da Siriya.
Hazali ya ce, "Amurka ta nuna ba ta girmama jinin mutanen Iraki, zubar da jinin matasanmu zai janyo zubar da jinin sojojin Amurka 'yan mamaya."
Hazali ya kara da cewa, idan Amurka ta ci gaba da kaiwa mayakan Hashdi Sha'abi hari to su ma za su ci gaba da kai musu.
A ranar Lahadi 27 ga Yuni ne Amurka ta kaiwa tsagerun Hashdi Sha'abi hari ta sama a kan iyakar Iraki da Siriya. Kungiyar ta bayyana mutuwar mambobinta 4.
Manyan Shugabannin tsagerun Shi'a ne suka halarci jana'izar mayakan 4 da aka kashe wanda aka gudanar a Bagdad Babban Birnin Iraki.