Wannan ya biyo bayan tsawon lokacin da aka dauka ana mahawara da kuma shiga tsakanin bangarorin biyu dake rikici wadda kasar Qatar ke jagoranci.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce daga cikin yahudawa 33 da ake saran Hamas ta fara saki, wadanda 5 daga cikin su sojoji ne mata, Isra'ilar za ta saki Falasdinawa 50 da take tsare da su, cikin su harda wadanda aka daure a gidan yari da wadanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai.
Yarjejeniyar ta ce a cikin kwanaki 42 na farko bayan amincewa da yarjejeniyar, sojojin Isra'ila za su janye daga anguwannin jama'a, yayin da za'a bai wa Falasdinawa damar komawa gidajen su a arewacin Gaza tare da kai musu kayan agaji wanda zai kunshi motoci 600 kowacce rana.
Ana saran bangarorin biyu tare da masu shiga tsakani sun amince da wani sabon daftarin mataki na 2 na yarjejeniyar bayan fara aiki da wannan na farko.
A karkashin yarjejenitar ta farko, Isra'ila za ta ci gaba da kula da mashigin Philadelphi wanda ke iyakar Gaza da Masar duk da bukatar kungiyar Hamas na janye dakarunta a wurin, yayin da ta amince ta janye sojojin ta dake mashigin Netzarim.
Yarjejeniyar ta 2 zata kunshi bukatar Hamas ta saki daukacin sojojin Isra'ilar da take garkuwa da su domin ganin an saki wasu karin Falasdinawan da ake tsare da su.
Sai dai Hamas tace ba zata saki sauran mutanen da tayi garkuwa da su ba muddin Isra'ila bata kawo karshen yakin ba.
Rahotanni sun ce yarjejeniya ta 3 zata mayar da hankali a kan musayar gawarwakin sauran mutanen da aka yi garkuwa da su domin bada damar sake aikin gina Gaza na shekaru 3 zuwa 5 a karkashin jagorancin kasashen duniya.
Shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden da wanda zai gaje shi Donald Trump duk sun tabbatar da zuwa karshen tattaunawar zaman lafiyar nan kusa da kuma kulla yarjejeniya a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI