Tsagaita wuta ba shi ne zai kawo karshen matsalar Falasdin-Isra’ila ba

Tsagaita wuta ba shi ne zai kawo karshen matsalar Falasdin-Isra’ila ba

Masanin diflomasiyya a Falasdin ya bayyana cewa tsagaita wuta kawai ba zai kawo karshen matsalar yankin ba, har sai an samar da kasar Falasdinawa mai ‘yanci.

Ministan harkokin wajen Falasdin Riad Al-Malki ya bayyanawa manena labarai cewa tsagaita wuta mataki ne mai kyau amma ba zai magance matsalolin dake kasa ba. Ba zai kawo karshen cin zarafin da mamayar da Isra’ila ke yiwa yankin Falasdinawa ba.

Ya kara da cewa matukar ana bukatar kawo karshen matsalar ya kamata a dauki matakan hana Isra’ila mamayar yankin Falasdinawa da kuma taka mata burki akan korar Falasdinawa da take yi daga gidanjensu.

Haka kuma ya zama wajibi a ja kunnen akan farmakan da Isra’ila ke kaiwa a yankin Masjid al Aqsa da Sheikh Jarrah.


News Source:   ()