Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rataba hannun akan dokar da zata haramta kafar sanar da zumuntar kasar China mai suna TikTok.
Trump, dake dawowa daga ziyarar da yakai Florida ya yi jawabi bayan saukarsa a babban birnin kasar Washington.
Mun dauki tsawon lokaci muna nazari akan kalubalantar kafar sadar da zumuntar TikTok inji Trump, ya kuma kara da cerwa,
"Zamu haramta TikTok a Amurka."
Da yake jaddada cewa a halin yanzu yana da ikin daukar mataki na gaggawa akan tattalin arziki, Trump ya nanata cewa ko dai ya yi amfani da wadannan ikon ko kuma ya sanya hannu kan dokar shugaban kasa na haramta TikTok.