Wannan na zuwa ne, yayin da Trump ke karbar bakuncin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, inda ake ganin baya ga batun makomar Falasdinu a Gaza da za su tattauna a kai, akwai batun makomar takunkuman da ke kan Iran din.
Matakin Mista Trump dai ya dawo da tsauraran manufofin Amurka kan Iran da shugaban na jam'iyyar Republican ya yi a tsawon wa'adinsa na farko, bayan ya zargi gwamnatin tsohon shugaba Biden da sassautawa kasar.
Hasashen da aka yi kan danyen man da Iran ke fitarwa ya kai matsayi mafi girma a shekarar 2024 yayin da kasar ta yi watsi da takunkumin da aka kakaba mata, musamman a bangaren samar da kudaden shiga, in ji wata sanarwa da fadar gwamnatin Amurka ta fitar.
A shekarar 2023, Iran ta samu dala biliyan 53 a bangaren mai, da dala biliyan 54 a shekarar 2024, a cewar alkaluman Hukumar Kula da Makamashi ta Amurka.
A wa’adinsa na farko, Trump ya nemi yin amfani da tsauraran takunkumai don murkushe tattalin arzikin Iran tare da tilastawa kasar mika wuya kan kudurorin da aka bijiro mata da su game da shirinta na nukiliya.
Jami'an diflomasiyyar Turai da na Iran sun gana a watan Nuwamba da Janairu don kan ko za su iya yin aiki don kwantar da tarzomar yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun nukiliyar kasar, kafin Trump ya dawo kan karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI