Lamarin mai cike da ban mamaki ya janyo caccaka daga Saudiya wadda Trump ke fatan za ta ƙulla alaƙa da Israila.
Wani jami’i daga ofishin Hamas Sami Abu Zuhri, wanda ya shugabanci yankin Gaza kafin faro rikicin Israila, ya faɗawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa furucin Trump na ƙwace Gaza shirme ne.
Trump ya faɗi wannan shirin nasa ne ba tare da ya yi bayanin taƙamaimai abinda zai yi ba, yayin wani taro a jiya Talata tare da Fira Ministan Israila Benjamin Netanyahu da ke ziyara a Amurka.
Trump ya shaida wa manema labarai cewa, Amurka za ta kwace Gaza tare da gina shi ta hanyar samar wa dubun dubutar mutane aiki, kuma zai zama matakin da idan ya ɗauka zai faranta wa kafatanin yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da buƙatar kwashe Falasɗinawa sama da milyan 2 daga zirin Gaza zuwa ƙasashe makwabta, a wani yanayi da ake tsaka da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Israila da Hamas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI