Acewar Donald Trump, idan har Canada ta koma ƙarƙashin Amurka ko shakka babu za ta samu garkuwa daga barazanar ƙasashe irin China da Rasha, haka zalika ƙasar ba za ta fuskanci sabbin haraji kan kayakin da ta ke sarrafawa ta ke kuma shigarwa ƙasar ta Amurka ba.
Donald Trump wanda ke gab da shan rantsuwar kama aiki, ya ce idan har Canada ta koma cikin gamayyar Amurka, babu ko da ƙasa guda ta ita ya iya yi mata barazana saɓanin halin da ta ke ciki a yanzu, ta yadda jiragen China da Rasha ke ci gaba da shawagi a iyakarta.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Donald Trump ke irin wannan kira ga Canada ba, domin ko a wa’adinsa da ya gabata ya buƙaci maƙwabciyar tasu ta koma ƙarƙashin don kara ƙarfin Washington.
A Litinin ɗin da ta gabata ne, Justin Trudeau ya sanar da murabus daga kujerar mulkin Canada wanda ya kawo ƙarshen matsin lambar da ya ke fuskanta daga jam’iyyar da ke ganin mummnan koma baya ƙarƙashin mulkinsa na shekaru 9.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI