Trump ya rage tazarar da Harris ta bashi tsakanin Amurkawa

Trump ya rage tazarar da Harris ta bashi tsakanin Amurkawa

Sabbin alƙaluman binciken kamfanin dillancn labarai Reuters, sun nuna cewar a halin yanzu ratar da ke tsaknain Trump da Harris a tsakanin Amurkawa Hispanic maza ta ragu ne zuwa kashi 2, wato tsohon shugaban na da magoya baya daga cikinsu kashi 44, yayin da Harris ke da kashi 46.

A watan Oktoban 2020, ratar kashi 19 ɗan takarar Democrats kuma shugaba mai ci Joe Biden ya bai wa Donald Trump, a tsakanin Amurkawan masu alaƙa da Spain.

Ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a ƙarƙshin haɗin gwiwar kamfanin dillancin labarai Reuters da cibiyar Ipsos mai binciken ra’ayoyin jama’a dake da hedikwata a Paris, ta nuna cewar duk da ana tafiya kankankan tsaknain Harris da Trump dangane da samun karɓuwa tsakanin Amurkawa masu zaɓe, ‘yar takarar ta Democrats ke kan gaba da kashi 46 cikin 100, yayin da ɗan takarar Republican ke da kashi 43.

Sai dai ƙwararrun da suka gudanar da kuri’ar jin ra’ayin sun ce mai yiwuwa akwai kuskure, ko kuma a ga saɓanin sakamakon da suka fitar da kwatankwancin kashi 2 zuwa 6. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)