Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rataba hannu akan wasu dokokin hudu da zasu bayar da damar rage kudin magani a kasar.
Gabanin rataba hannun Trump ya yi jawabi a fadar White House inda ya bayyana cewa majalisar kasar ta dauki tsawon lokaci tana son ta rage farashin magani a kasar amma har ila yau ba'a cimma matsaya ba.
"Ni ba zan kara jira ba, sabili da haka ina mai rataba hannu akan dokoki hudu da zasu rage farashin kudin magani sosai a kasar"
Trump, ya kara da cewa a cikin shekaru 51 wannan ne karon farko da ake rage kudin magani a kasar sai dai wannan bai kai ga matsyar da ake bukata ba.
A yayinda yake tsokaci akan yaki da kwayar cutar Covid-19 ya bayyana cewa abu mafi muhinmaci da ya kamata a cimma shi ne samar da allurar riga-kafi.