
Lamurra sun fara dagulewa ne tun bayan da Donald Trump ya yi gaban kansa wajen fara jagorantar tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine ba tare da gayyatar Kiev ba, ciki kuwa har da tattaunawa da Putin ta wayar tarho, a wani yanayi da yaƙin ke gab da cika shekaru 3 da farowa wanda ke matsayin mafi muni da nahiyar Turai ta gani tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Tun a jiya Laraba ne Donald Trump ya bayyana cewa ya dace Zelenskiy ya yi gaggawar amincewa da kawo ƙarshen yaƙinshi da Rasha ko kuma ya iya rasa ƙasar da zai jagoranta, kalaman da tuni suka haddasa cece-kuce a ciki da wajen nahiyar ta Turai.
Cikin masu kakkausar suka ga Trump har da Jam'iyyar Democrat mai adawa sai kuma wasu daga mambobin Jam'iyyar Republican da ke ganin sam bai dace shugaban na Amurka ya yi barazana ga wani shugaba ba.
Kai tsaye Trump ya ɗora laifin mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine kan Zelenskiy, wanda ya ce tun farko shi ya haddasa matsalar, maimakon warware rikicin ta ruwan sanyi, kalaman da tuni fadar gwamnatin Kiev ta yi martani akansu, a wani yanayi da bayanai ke cewa yanzu haka kashi 20 na ƙasar ya kufce daga hannunta.
Trump wanda ya kira Zelenskiy da ''ɗan barkwanci mai nasara'', ya ce babu ta yadda za a yi Amurka ta amince da buƙatar ɗan wasan barkwanci wajen zuba maƙuden kuɗi har dala biliyan 350 a yaƙin da babu yadda za a yi ta samu nasara.
Daga lokacin da Rasha ta faro mamaya a Ukraine kawo yanzu, Amurka ta kashe kuɗin da ya kai dala biliyan 183 yayinda ƙasar ta gabashin Turai ta gaza gudanar da zaɓen da bisa ƙa’ida ya kamata ayi cikin watan Aprilun 2024.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI