Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana nada shahararren likita dan asalin kasar Turkiyya mai tiyatar zuciya Dr. Mehmet Oz a matsayin memba a Cibiyar Wasanni, Kwarewa da Ciyarwa.
Dangane da sanarwa da fadar White House ta sanar a rubuce, shugaban Trump ya fitar da jerin sunayen da zai nada a Cibiyar Wasanni, Kwarewa da Ciyarwa.
Daga cikin sunayen 29 akwai likitan zuciya dan ainihin kasar Turkiyya mazauni a birnin New Jersey Dkt. Mehmet Oz.
Cibiyar da shugaban kasar Amurka na 34 Dwight David Eisenhowe ya kafa a shekarar 1956 na taimakawa Amurkawa wajen kwarewa akan wasanni, karin lafiya da cin abinci masu gina jiki.