Trump ya lashe lambar yabo ta 'gwarzon shekara'

Trump ya lashe lambar yabo ta 'gwarzon shekara'

 

Trump ya fara zama gwarzon shekara ne na wannan mujallar a 2016 bayan ya lashe zaɓen Amurka da aka gudanar a wancan lokaci.

A wani sako da ya aike wa masu karatu, shugaban mujallar Sam Jacobs ya bayyana Trump a matsayin wanda ya jajirce wajen tsara sake komawarsa kan karagar mulkin Amurka.

Zaɓaɓɓen shugaban na Amurka na jam'iyyar Republican ya kaɗa kararrawar da ke alamta kaddamar da buɗe hada-hada a kasuwar hannayen jari ta New York a wannan Alhamis domin nuna farin cikinsa da karramawar, inda ya samu rakiyar iyalansa da wasu mukarrabansa da ke ta furta "U-S-A".

A hirarsa da Mujallar ta Times, Trump ya sake jaddada wasu daga cikin matakan da zai aiwatar da zaran ya sha rantsuwar kama aiki a matsayinsa na sabon shugaban Amurka a cikin watan Janairu mai zuwa.

Bankon Mujallar Time ɗauke da hoton Trump Bankon Mujallar Time ɗauke da hoton Trump © AP/Alex Brandon

Ya yi alkawarin sake duba tuhumar da ake yi wa magoya bayansa da suka gudanar da zanga-zanga tare da kutsawa cikin ginin Majalisar Dokokin Amurka a watan Janairun 2021, duk da cewa a can baya ya ce, kai tsaye zai yi musu afuwa.

Kazalika ya yi alkawarin samar da ƙarfin tattalin arziƙin da babu wanda ya taɓa garin irinsa a Amurka, yana mai alwashin zabtare kuɗaɗen haraji da kaso mai yawa.

Tun shekarar 1927 ne Mujallar Time ta fara karrama gwarzon shekara, inda take bada lambar yabo ga mutum ko kuma ƙungiya saboda taka rawa a wani ɓangare ko kuma gamuwa da ibtila'i.

Daga cikin waɗanda suka taɓa lashe lambar yabon a baya-bayan nan har da tsohon shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Kamfanin Meta mai kula da shafin Facebook, Mark Zuckerberg da Fafaroma Francis da kuma shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.

Editocin Mujallar Time ne ke yanke shawarar wanda ya cancanci lashe kyautar a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)