Donald Trump ya ba da wannan tabbacin ne a jiya litinin na cewar Vladimir Putin zai amince da kasancewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Turai a Ukraine, inda shima shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ba da tabbacin cewa kasashen Turai a shirye suke wajen ba da tasu gudun-mawar.
A yayin da shugaban na Amurka ke amsa tambaya daga manema labaru ya bayyana cewa babu wani kokwanto da yake dashi akan takwaransa na Rasha Vladymir Puttin akan rungumar tsarin na ƙasashen turai.
Sai dai in ba a mance ba a wani taro da ya gudana na neman mafita kan yaƙin na Ukraine, wanda ya gudana a ƙasar Saudiya ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa, ba zasu amince da wani Tsarin dakaru ko na sojojin kasashen NATO, amma a karkashin tutar kasashen waje ba.
To amma a ranar Litinin ɗin nan, a wata ganawar Trump a Ofishinsa na Oval tare Emmanuel Macron ya bayyana cewa kasashen Turai a shirye suke su aika da sojoji don tabbatar da ganin ana mutunta juna ta hanyar zaman lafiya sosai, tare da ba da tabbacin Turai a shirye take ta kashe maƙudan kuɗi wajen tabbatar da tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI