Trump na yunkurin fitar da Amurka daga Hukumar WHO

Trump na yunkurin fitar da Amurka daga Hukumar WHO

Gwamnatin shugaba Donald Trump ta sanar da majalisan dattawan kasar anniyarta na fitar da kasar Amurka daga cikin Kungiyar Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO.

Sanatan New Jersey kuma shugaban kwamitin huldan kasa da kasa Bob Menendez,ya yada a shafins ata Twitter da cewa sabuwar kwayar cutar Covid-19 na cigaba da addabar duniya Inda ya kara da cewa:

"A yayin da ake fama da wacannan annobar majalisa ta samu sanarwa daga shugaba Trump akan yunkurin fitar da Amurkja daga Hukumar Lafiya ta Duniya"

Menendez, ya kara da cewa wannan matakin na gwamnatin Trump zata jefa Amurka cikin 'Rashin lafiya da kadaici"

 


News Source:   www.trt.net.tr