Yayin ganawa da manema labarai bayan tattaunawar sirri da shugabannin biyu suka yi, an samu tada jijiyoyin wuya da kuma mahawara mai zafi tsakanin shugabannin dangane da kawo ƙarshen yakin.
Da farko mataimakin shugaban Amurka J.D, Vance da ke wurin ya zargi shugaba Zelensky da rashin mutunta Amurka dangane da ƙokarin da suke yi na kawo ƙarshen yakin, lokacin da ya bayyana cewar suna buƙatar tabbacin ba su kariya daga Rasha.
Waɗannan kalamai sun daɗa zafafa Trump wanda ya zargi Zelensky da ƙoƙarin kaucewa batutuwan da suke faruwa a ƙasarsa, da suka haɗa da gazawar ƙarfin tinkarar Rasha a yaƙin da kuma irin koma bayan da Ukraine ke samu.
Trump ya ce inda ba don taimakon Amurka ba, da tuni Rasha ta murƙushe Ukraine, saboda haka ya zama wajibi Zelensky ya godewa Amurka da kuma irin gudunmawar da take bai wa ƙasarsa musamman a halin yanzu na ƙoƙarin kawo ƙarshen yakin.
Shugaba Trump ya ce kuskure ne Zelensky ya ce ba zai ƙulla yarjejeniyar kawo karshen yaƙin ba har sai ya samu abin da yake so, yayin da ya ƙara da cewa muddin ba zai mutunta ƙoƙarin da suke na sasanta rikicin ba, Amurka na iya janyewa, kuma ya san Rasha na iya mamaye Ukraine.
Ƙoƙarin gabatar da buƙatar da Ukraine ke da shi game da kawo ƙarshen yakin, bai samu goyan bayan Trump da mataimakinsa Vance ba a wajen ganawar, inda akayi ta samun kalaman shugaban na karo da juna lokacin ganawar, abin da ya kai ga Trump na bayyana cewar Zelensky na yunƙurin ko kuma wasa da barkewar yakin duniya na 3.
Zelensky ya ce tun daga shekarar 2014 lokacin shugaba Barack Obama shugaban Rasha Vladimir Putin ya ke kai wa ƙasarsa hari da kuma ƙwace yankunan ta ba tare da ƙaƙƙautawa ba, saboda haka yana buƙatar samun tabbacin tsaro daga Amurka, kuma waɗannan kalamai ba su yiwa Trump dadi ba.
Nan take shugaban na Amurka ya kira tsohon shugaban Amurka Joe Biden a matsayin shashashan shugaba, saboda abinda ya kira Dala biliyan 350 da Amurka ta kashe wajen tallafa wa Ukraine akan yakin da ta shiga da Rasha, yayin da shi Zelenski ke ikrarin cewa duniya taki taimaka masa.
Shi dai Zelensky na Amurka ne domin ƙulla yarjejeniyar bai wa Amurka damar haƙar ma'adinai a ƙasarsa domin taimaka masa wajen yaƙin da aka kwashe shekaru 3 anayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI