Trump bai isa ya koreni daga kujarata ba -Shugaban babban bankin Amurka

Trump bai isa ya koreni daga kujarata ba -Shugaban babban bankin Amurka

Jerome Powell ya ce ba zai sauka ba idan Trump ya nemi ya yi hakan, kuma bisa tsarin dokar kasar, babu wanda ya isa ya tilasta masa sauka daga kan wannan mukami.

Mista Powell yana amsa tambayoyi ne a wani taron manema labarai bayan bankin ya sanar da rage kudin ruwa na lamuni.

Masu hasashe sun yi tsammanin farashin lamuni zai kara faduwa a watanni masu zuwa amma sun yi gargadin cewa shirin Trump akan haraji, shige da fice da dai sauransu na iya ci gaba da matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma kara rancen da gwamnati ke karba.

Trump ya yi alkawarin sanya harajin shigo da kaya na akalla kashi 10 cikin 100 kan duk kayayyakin da aka shigar da su cikin kasar, abin da masana tattalin arziki suka ce zai fi aiki ne kan masu saye, wato babu abin da zai haifar face tayar da farashi.

Har ila yau, karin haraji na iya haifar da hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar yawan kashe kudade, yayin manufar korar bakin haure da Trump ya gabatar zai haifar da wani babban gibi ga ma’aikatu a Amurka wanda zai iya haifar da karin albashi.

Kudin ruwa na bashin da ake bin Amurka ya ninka a wannan makon, Wanda sima masana suka ce abin damuwa ne.

Mista Powell ya fada a ranar Alhamis cewa ya yi da wuri don bayyana yadda ajandar sabuwar gwamnatin za ta iya shafar tattalin arzikin Amurka ko kuma abin da baitul malin kasar  ya kamata ya yi na tunkarar matsalolin tattalin arziki.

A lokacin wa'adinsa na farko, Trump ya kira jami'an banki da masu taurin kai a shafukan sada zumunta kuma an ce ya tuntubi masu ba da shawara kan ko zai iya korar Mista Powell a wancan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)