Tinubu zai kai ziyara Faransa bisa gayyatar da shugaba Macron ya masa

Tinubu zai kai ziyara Faransa bisa gayyatar da shugaba Macron ya masa

Onanuga ya ce ziyarar kwanaki uku za ta mayar da hankali ne wajen kara ƙulla alaƙar siyasa, tattalin arziƙi, al’adu da ƙulla yarjejeniyoyi a fannin noma, tsaro, ilimi, lafiya da samar wa matasa ayyukan yi da sauran abubuwan da za su kawo ci gaban ƙasashen biyu.

Za’a yi bikin tarbar shugaba Tinubu da uwar-gidansa Sanata Oluremi Tinubu a gidan ajiyar kayan tarihin sojin Faransa mai shekaru 350 da ke cikin fadar shugaban ƙasar, kuma zai samu tarba daga shugaba Macron, da uwar-gidansa Brigitte.

Yayin ziyarar, Tinubu da Macron za su fi tattaunawa kan  haɗin gwiwar ayyuka, musamman a ɓangaren matasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugabannin biyu za su kulla alaƙar kuɗaɗe, albarkatun ƙarƙashin ƙasa, kasuwanci da kuma zuba jari.

Brigitte da Oluremi za su tattauna kan tallafawa mata, ƙananan yara da masu ƙaramin ƙarfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)