Tinubu ya taya Donald Trump murnar sake lashe zaben Amurka

Tinubu ya taya Donald Trump murnar sake lashe zaben Amurka

Mashawarcin shugaban na musamman kan al’amuran kafafen yada labarai, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaba Tinubu na fatan karfafa dangantakar dake tsakanin Najeriya da kuma Amurka.

A cewar shugaba Tinubu, nasarar da Trump ya samu na tabbatar da irin amannar da ‘yan kasar suka yi a kansa, musamman wajen gudanar da shugabanci na gari.

Ya kuma yabawa al'ummar Amurka bisa irin jajircewarsu wajen bawa tsarin dimokradiyya gudun mowar da ta dace.

Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa, idan aka yi la’akari da kwarewar Shugaba Trump a matsayin shugaban Amurka na 45 daga 2017 zuwa 2021, komawar sa fadar White House a matsayin shugaban kasa na 47 zai haifar da ci gaban tattalin arziki, da kuma aiwatar da ayyukan hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki, musamman ma tsakanin Amurka da kuma kasashen Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)