Hukumar Hadin Kai da Kulawa ta Turkiyya (TIKA), ta taimakawa gidan marayun dake lardin Sar-i Pul a arewacin kasar Afghanistan da kayayakin amfanin yau da kullum.
Kamar yadda bayanai suka fito daga ofishin TIKA dake Mezar-ı Şerif, an taimakawa yara 60 dake gidan marayun garin Sar-i Pul da gadaje, barguna, sutura da makamantansu.
TIKA wacce ta farantawa dukkanin yaran dake gidan marayun Sar-i Pul rai, ta bayyana cewa ya kamata gidan marayun ya zama irin na zamani ta yarda zai kasance da dukkanin komai da yaran ke bukata.