Tianwen-1 da China ta harba ya bar duniya da nisan kilomita miliyan 15

Tianwen-1 da China ta harba ya bar duniya da nisan kilomita miliyan 15

Na'urar tauraron dan adam dın Tianwen-1 da China ta harba a watan Yuli zuwa sararin samaniya da zummar gudanar da bincike a duniyar Mars ya yi tafiyar nisan kilomita miliyan 15 daga Duniya.

Hukumar Harkokin Sararn Samaniyar kasar China a farkon watan Agusta ta bayyana cewa na'uarra tauraron dan adam dın Tianwen-1, da ta harba na cigaba da tafiya dai-dai.

Ana dai hasashen cewa tauraron dan adam din mai suna Tianwen-1 da a halin yanzu ya bar duniya da nisan kilomita miliyan 15 zai sauka a duniyar Mars a watan Febrairun shekarar 2022.

A lokacin da na'urar Tianwen-1 ya isa jar duniyar, zai kasance ya yi tafiyar kilomita miliyan 470.

 


News Source:   ()