Tawagar Tarrayar Turai ta ziyarci Yemen akan samar da zaman lafiya

Tawagar Tarrayar Turai ta ziyarci Yemen akan samar da zaman lafiya

Wata tawaga daga Tarayyar Turai (EU) ta je Aden babban birnin wucin gadi don tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya tare da sabuwar gwamnati a Yemen.

Bayanai daga majiyoyin gwamnati na nuna cewa, EU na yin irin wannan ziyarar a karon farko tun bayan da sabuwar majalisar ministocin ta isa kasar daga Saudiya a ranar 30 ga Disamban 2020.

Tawagar ta EU ta hada da jakadu a Yemen daga Faransa, Netherlands, Belgium, Norway, Jamus, Finland, Sweden da Ireland.

Tawagar da ta isa birnin Aden sun tattauna da firaiminista Muhin Abdullmalik da ministan harkokin waje Ahmad Awad Bin Mubarak a fadar Meashik akan yunkiurin samar da zaman lafiya.

 


News Source:   ()