An kamamla zaman farko tsakanin dakarun kasashen Turkiyya da Girka a zauren kungiyar NATO.
Ma'aikatar Harkokin wajen Turkiyya ce ta bayyana cewa an kammala zaman tattaunawa tsakanin dakarun Turkiyya da Girka a zauren Hukumar NATO kuma za'a sake wani zaman a ranar 17 ga watan Satumba.
An yanke hukuncin zaman tattaunawa tsakanin tawagar dakarun Turkiyya da na Girka ne a zauren Hukumar NATA bayan tattaunawar da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya yi da Babban Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg.
Kasashen biyu sun yi zama na farko a zauren NATO a kan lamurkan rabon yankunan a ranar 10 ga watan Satumba.