Tattaunawar zaman lafiya babu Ukraine ba zai haifar da ɗa mai ido ba - Zelensky

Tattaunawar zaman lafiya babu Ukraine ba zai haifar da ɗa mai ido ba - Zelensky

Zelensky ya ce idan har ana son cimma matsaya da za ta kawo ƙarshen yaƙin, to ya zama dole a sanya Ukraine cikin tattaunawar zaman lafiyar.

Furucin nasa na zuwa a matsayin martani ga jita-jitar da ake yaɗawa na yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin na kusan shekaru 3, da ya laƙume rayukan dubban jama’a tare da jikkata wasu da dama.

A farkon makon nan ne, shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya ce a shirye yake domin shiga tattaunawa da sabon shugaban Amurka, Donald Trump kan Ukraine, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai basira da zai iya daƙile barkewar yaƙin tun sanda aka faro shi a watan Fabrairun 2022.

Putin dai bai bayyana lokacin da za’a gudanar da zaman ba, kana fadar Kremlin ta ce har yanzu ta na jiran kira daga Washington, duk da cewa Trump ya sanar a ranar Alhamis cewa zai iya ganawa da Putin nan take.

Trump wanda aka rantsar a ranar Litinin da ta gabata, ya bayyana rikicin na Ukraine a matsayin abun dariya, har ma ya yi barazanar ƙaƙabawa Rasha takunkumai idan ba ta amince da dakatar da yaƙin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)