Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya tattauna da sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg ta wayar tarho.
Kamar yadda ma'aikatar sadarwar kasar Turkiyya ta sanar shugaba Erdoğan ya tattuana da Stoltenberg inka aka taba batun Gabashin Bahar Rum da kuma bayyana cewa Turkiyya zata ci gaba da daukar matakan kare hakkokinta a koda yaushe.
Erdoğan, ya bayyana cewa Turkıyya na goyon bayan matakan da zasu sanya ko wace kasa a yankın Bahar Rum ta samu nasara ta hanyar bın doka da ka'ida. Ya kuma nanata cewa duk wata yunkurin da zai sabawa dokar kasa da kasa da kuma abinda zai haifar da hasara a yankin ya zama wajibi ga kungiyar NATO ta yi abinda ya dace akai.